Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle, ya karyata rahotannin da ke cewa ya bada gudunmawar naira miliyan 100 domin gina jami’a a jihar Jigawa.
Mai Magana da yawun gwamnan Zailani Bappa ya karyata rahoton, inda ya ce gudunmawar da Matawalle ya bada gudunmawa ce ga kungiyar Izala da ke gina babbar makaranta a jihar.
Idan dai ba a manta ba, an wallafa labarin yadda Matawalle ya ba shugaban kungiyar Izala Sheikh Bala Lau gudunmawar naira miliyan 100, domin ci-gaba da ginin wata makaranta da kungiyar ke ginawa a garin Shinkafi.
Zailani Bappa, ya ce babu abin da ya hada gudunmawar Matawalle da jihar Jigawa, kungiyar Izala aka ba domin kammala makarantar da su ke ginawa a Shinkafi, wadda ake sa ran ta zama jami’ar musulunci nan gaba.

