Home Labaru Martani: Jonathan Ya Ce Nijeriya Ba Za Ta Rabu Ba Bayan Zaɓen...

Martani: Jonathan Ya Ce Nijeriya Ba Za Ta Rabu Ba Bayan Zaɓen Shekara Ta 2023

107
0
Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya yi watsi da fargabar da ake yi cewa Nijeriya za ta rabu bayan zaben shekara ta 2023.

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya yi watsi da fargabar da ake yi cewa Nijeriya za ta rabu bayan zaben shekara ta 2023.

Jonathan ya bayyana haka ne, yayin wani taron kara wa juna sani da Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma na Dattawa ta shirya a Legas, inda ya ce hasashen da aka yi a baya cewa Nijeriya za ta rabu ba zai zama gaskiya ba.

Goodluck Jonathan, ya ce ya na kyautata zaton za a yi zabe na adalci a shekara ta 2023.

Ya ce yayin da ke mulki a lokacin zaben shekara ta 2015, wasu sun rika maganganu zuwa kasashen waje, amma babu abin da ya faru daga karshe, don haka zaben shekara ta 2023 zai zo ya wuce kuma Nijeriya ba za ta rabu ba.