Gogaggiyar ‘yar siyasa kuma mai kare hakkin ɗan Adam Naja’atu Mohammed, ta yi kira ga rundunar tsaron Nijeriya su gaggauta kama uwargidan shugaban kasa A’isha Buhari, bisa kama dalibin da tasa aka yi sannan ta rika jibgar sa.
Idan dai ba a manta ba, A’isha Buhar ta sa an kama wani matashin ɗaliɓi saboda ya sanya rubutun da ya shafe ta a shafin tiwita.
Naja’atu Mohammed ta nuna bacin ran ta, tare da yin kira ga A’isha Buhari da kakkausar murya cewa ta gaggauta sakin matashin, sannan rundunar tsaron Nijeriya su kama ta a kuma tsare ta
Ta ce babu yadda za a ce irin waɗannan matasa da suka zaɓi mijin A’isha Buhari a matsayin shugaban kasa, kuma a ce za a rika yi masu da sauran jama’a mulkin kama karya.
Naja’atu ta kara da cewa, ‘yan Nijeriya Buhari su ka zaɓa ba A’isha Buhari ba, don haka karya doka ne ta rika amfani da karfin kujerar shi ta na ci wa mutane mutunci yadda ta ke so.