Home Labaru Martani: Gwamnatin Nijeriya Ta Karyata Zargin Kuntata Wa Kiristoci

Martani: Gwamnatin Nijeriya Ta Karyata Zargin Kuntata Wa Kiristoci

396
0
Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin tarayya ta karyata zargin da Kungiyar Dattawan Kiristocin Arewa ta yi wa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari cewa za ta kuntata wa Kiristocin kasar nan.

Bayanin hakan ya na kunshe ne a cikin wata wasika da Jakadan Nijeriya a Birtaniya George Oguntade ya aike wa wasu ‘yan Majalisar kasar. A cikin wasikar, Gwamnatin Nijeriya ta karya ce da rashin tunani har wani ko wata kungiya ta ce kungiyar Boko Haram shiri ne da gwamnati ke amfani da shi a kan Kiristocin Nijeriya.

Oguntade, wanda tsohon mai shari’a ne a Kotun Koli na Nijeriya, ya aika martanin ne ga Ofishin Harkokin Wajen Birtaniya Mai Lura da Batutuwan Zargin Takura Wa Kiristoci a Kasashe Rainon Ingila.

Ya ce Mataimakin Shugaban Kasa Kirista ne, kuma Shugaba Buhari ya kan yi tarurruka da shugabannin Kiristoci a ciki da wajen Nijeriya, sannan ministocin Nijeriya ma raba-daidai ake yi tsakanin Musulmai da Kirista, kuma shi kan sa baya ga cewa Kirista ne, Babban Jagora ne a Darikar Kiristocin Angalikan a Nijeriya.

Leave a Reply