Home Labaru Martani: Garba Shehu Ya Yi Masu Sukar Tafiye-Tafiyen Shugaba Buhari Raddi

Martani: Garba Shehu Ya Yi Masu Sukar Tafiye-Tafiyen Shugaba Buhari Raddi

308
0
Garba Shehu, Mai Taimaka Wa Shugaban Kasa Ta Fuskar Yada Labarai Da Hulda Da Jama’a

Mai taimaka wa shugaban kasa ta fuskar yada labarai da hulda da jama’a Garba Shehu, ya bayyana zuwa Umarar Shugaba Buhari a matsayin daukaka darajar Nijeriya a idon duniya.

Garba Shehu ya bayyana haka ne a matsayin martini, dangane da maganganun da wasu ‘yan Nijeriya ke yi a kan yawan tafiye-tafiye da Shugaba Buharike yi zuwa kasashen ketare, inda yace babu adalci a ce shugaba Buhari bai cika zama a kasar shi ba.

Shugaba Buhari dai ya bar Nijeriya zuwa kasa mai tsarki, biyo bayan gayyatar da sarkin Saudiyya Salman Bin Abdulaziz yayi mashi domin yin aikin Umarah. Umarar shugaba Buhari dai ta na zuwa, makonni biyu bayan mahukunta kasar Saudiyya sun sako Zainab Aliyu da suka zarga da safarar miyagun kwayoyi bayan ta shafe watanni hudu a tsare.