Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Martani: Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Wa Jaridar Punch Raddi

Fadar Shugaban Kasa ta yi raddi a kan bayanan da ke cewa salon mulkin kama-karya Shugaban kasa Muhammadu Buhari ke aiwatarwa a Nijeriya.

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa, shugaban Buhari ya yi kaurin suna wajen ta ke umarnin kotu, tun bayan hawan sa mulki a shekara ta 2015, da kuma yadda  kotu ta cin zarfin shugaban kamfanin sahara reportares Omoyele Sowore.

Jaridar ta wallafa wani rubutu mai taken “Matsayin Mu a kan Rashin bin doka da Oda da shugaban kasa Buhari ke yi, tare da cewa, ba za su sake kiran Buhari shugaban Kasa ba, sai dai su kira shi da Manjor Janar Muhammadu Buhari  mai ritaya.

Jaridar ta kara da cewa, wannan shine sunan da yafi dacewa da Buhari, duk da cewa a mulkin dimokradiyya aka zabe shi, amma ya ke gudanar, mulkin na kama-karya kamar lokacin mulkin soja.

Exit mobile version