Home Labaru Martani: Fadar Shugaban Kasa Ta Ce Gwamnati Ba Ta Hana Shigo Da...

Martani: Fadar Shugaban Kasa Ta Ce Gwamnati Ba Ta Hana Shigo Da Abinci Ba

570
0

Fadar Shugaban kasa ta yi karin haske kan matakin shugaban kasa Muhammadu Buhari, na hana bankin CBN ba masu shigo da kayan abinci Najeriya canjin kudi.

mai Magana da yawun Shugaban kasa, Malam Garba Shehu

A wani jawabi mai Magana da yawun Shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya yi ya ce shugaban kasa bai haramta ko sanya takunkumi akan shigo da abinci ba, dan haka fassarar jaridar financial Times kazafi ne.

Garba Shehu, ya ce babu wani haramci ko takunkumi da aka sanya kan shigo da abinci, domin kuwa har yanzu masu shigo da kayayyakin abinci na da damar neman canjin kudi daga hukumomi masu zaman kan su domin cigaba da harkokin su.