Fadar Shugaban kasa ta yi watsi da ce-ce-ku-cen da ake yi a kan rashin armashin bikin rantsar da shugaba Buhari da mataimakin sa a wa’adin mulki na biyu da aka yi ranar 29 ga Mayu.
Daya daga cikin manyan masu yawan sukar gwamnatin shugaba Buhari Injiniya Buba Galadima, ya ce rashin halartar shugabannin kasashen waje da tsofaffin shugabannin Nijeriya bikin, ya nuna cewa sun dawo daga rakiyar gwamnatin shugaba Buhari.
Sai dai mai ba shugaban kasa shawara ta fuskar yada labarai Garba Shehu ya maida martini da cewa, karairayi ne kawai da hassada ta wasu mutane.
Ya ce kwamitin shirya bikin ne ya bukaci shugabannin kasashen waje da duk wani bako daga waje ya bari sai narar 12 ga watan Yuni ya halarci bikin ranar dimokuradiyya ta Nijeriya.
Garba Shehu, ya ce kasashe 91 su ka nuna sha’war halartar bikin rantsar da shugaba Buhari, kuma yawancin su shugabannin kasashe ne da Firayin minista.
Ya ce ministocin harakokin waje ne mafi kankantar bakin da su ke tunani halartar bikin, sannan akwai shugabannin da su ka ce ko ba a gayyace su ba za su zo saboda shugaba Buhari.