Home Labaru Martani: Ban Hana ‘Yan Shi’a Yin Shi’ar Su Ba- Buhari

Martani: Ban Hana ‘Yan Shi’a Yin Shi’ar Su Ba- Buhari

658
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce umarnin da kotu ta bayar na dakatar da kungiyar Shi’a bai hana su gudanar da addinin su ba a Najeriya.

Kalaman shugaban kasa  na zuwa ne bayan hukuncin wata kotu a Abuja, da ta bayar da umarnin haramta kungiyar mabiya Ibrahim Zakzaky kamar yadda gwamnati ta nema.

Bayanan kotun sun nuna cewa gwamnati ta nemi a haramta kungiyar bayan ayyana ta a matsayin ta ‘yan ta’adda, inda ta zarge ta da haifar da asarar rayuka da dukiyoyi.

Mai magana da yawun kungiyar Ibrahim Musa ya yi watsi da zargin cewa suna tayar da husuma, sannan ya shaidawa kafar yada labarai  ta BBC cewar lauyoyi da jagororinsu na nazari kan umarnin kotun domin fitar da matsaya.

Kungiyar Shi’a

Mai magana da yawun shugaban kasa  Malam Garba Shehu, ya ce za a aiwatar da wannan hukunci na kotu domin haramta kungiyar shi’ a’ amma hakan ba yana nufin haramta Shi’a ba.

Malam Garba Shehu, ya ce akwai miliyoyin ‘yan Shi’a a Najeriya wadanda ke zaune lafiya kuma gwamnati ba ta da matsala da su, ba wanda zai tsangwamesu kuma suna harkokin su.

Leave a Reply