Tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo, ya nesanta kanshi daga labarin da ke yawo a shafukan sada zumunta cewar na goyon bayan masu shirya yi wa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari bore.
Namadi, ya ce ko kadan bashi bane ya mallaki wadannan shafuka da ke yada irin wadannan kalamai na batanci akan gwamnatin Buhari.
Ya kara da cewa ba zai yi kasa a gwiwa ba, wajen ganin an kama masu yada irin wadannan rade-radin da sunan sa domin a hukunta su.
Tsohon
mataimakin shugaban kasa, ya ce baya shiga shafukan sada zumunta, akan haka ya
bukaci daukacin al’ummar Najeriya su kauracewa karanta duk wani bayani wanda
aka sa sunanshi a shafukan sada zumunta na zamani.
You must log in to post a comment.