Home Labaru Martani: Atiku Ya Bayyana Ikirarin APC Na Cewa Shi Ba Dan Kasa...

Martani: Atiku Ya Bayyana Ikirarin APC Na Cewa Shi Ba Dan Kasa Ba Ne A Matsayin Sakarci

376
0
Atiku Abubakar, Dan Takarar Shugaban Kasa Na Jam’iyyar, PDP
Atiku Abubakar, Dan Takarar Shugaban Kasa Na Jam’iyyar, PDP

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya yi watsi da karar da jam’iyyar APC ta shigar da ke nuna cewa shi ba dan asalin Nijeriya ba ne.

Atiku Abubakar ya bayyana haka ne ta bakin mai magana da yawu sa Paul Ibe a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai, inda ya kara da cewa, wannan wani nau’i ne na cin mutuncin Atiku a idon ‘yan Nijeriya, duba da yadda  ya shafe tsawon shekaru takwas ya na a matsatin mataimakin shugaban kasa.

Atiku yak e ikirarin jam’iyyar APC sakarci ne kuma abun dariya ne, saboda Atiku Abubakar ya kasance tsohon mataimakin shugaban kasa baya.

Jam’iyyar APC dai ta shigar da kara kotun sauraran kararrakin zaben shugaban kasa da ke Abuja, inda ta ke cewa Atiku Abubakar ba dan Nijeriya ba ne, saboda haka bai cancanta ya yi takarar zaben shugaban kasa ba. Jam’iyyar APC ta yi ikirarin cewa, Atiku Abubakar dan kasar Kamaru ne, saboda haka kotu ta yi watsi da karar da ya shigar na kalubalantar nasarar da shugaba Muhammadu Buhari ya samu a zaben shekara ta 2019.