Home Labaru Martani: Atiku Abubakar Ya Karyata Jita-Jitar Da Ake Yadawa A Kan Shi

Martani: Atiku Abubakar Ya Karyata Jita-Jitar Da Ake Yadawa A Kan Shi

150
0

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, ya karyata jita-jitar da ke cewa ya dauko sojojin haya daga kasar Amurka don su taya shi kwatar kujerar shugaban kasa daga hannun shugaba Muhammadu Buhari.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Atiku Paul Ibe ya fitar, ya ce Atiku ya ce rahoton da aka fitar na karya ne ba shi da tushe balle makama, kuma yana da tabbacin cewa jam’iyyar APC ce ta fitar jita-jitar.

Mista Paul ya kara da cewa, jam’iyyar APC yanzu ta na zaune ne cikin fargabar tsoron kada a tona masu asiri, shi ya sa su ke amfani da labarun karya domin su bata wa Atiku suna maimakon su maida hankali wajen kare kan su a kotu. Ya ce karar da Atiku ya kai ta zame masu babbar barazana, shi ya sa su ke yada labarun bogi domin su kawar da hankulan jama’a akan irin magudin da su ka yi a zaben da ya gabata.