Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Martani: APC Ta Yi Tir Da Harin Da Aka Kai Wa Oshiomole A Jihar Edo

Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomole

Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomole

Jam’iyyar APC ta yi Allah-Wadai da harin da aka kai gidan Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole.

An dai kai harin ne a ranar Asabar da ta gabata, lamarin da ake zargin ‘yan bangar siyisa da ‘yan daba ne su ka kai harin.

Yayin da su ka kai harin a gidan sa da ke unguwar Okoroutun da ke birnin Benin na Jihar Edo, maharan sun rika rera wakar ‘Oshiomhole Barawo’, kafin daga bisani jami’an tsaro su tarwatsa su.

Sai dai a cikin wata sanarwa da kakakin yada labarai na jam’iyyar APC Lanre Issa-Onilu ya fitar, ya yi tir da harin tare da bayyana shi da cewa hari ne aka kai da nufin kashe Oshiomole.

Ya ce jami’an ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro na ci-gaba da bincike, kuma tuni sun bukaci Shugaban ‘yan Sandan Nijeriya da sauran jami’an tsaro su binciki lamarin, domin hukunta wadanda su ka dauki nauyin kai harin da wadanda su ka kai.

Exit mobile version