Home Home Manoman Najeriya Sun Tafka Asarar Naira Biliyan 577

Manoman Najeriya Sun Tafka Asarar Naira Biliyan 577

1
0

Hukumar Kididdiga ta kasa, ta ce bangaren noma ya tafka asarar naira biliyan 577 sakamakon ambaliyar ruwa da ta mamaye jihohin Nijeriya da dama a shekarar da ta gabata.

Gwamnatin tarayya, ta ce an bayyana adadin makuden kudaden da aka tafka asara a cikin wani rahoton Hukumar, wanda kawo yanzu ba a fitar da shi a hukumance ba.

Babban Jami’in Bada Alkaluma na kasa Semiu Adeniran, ya ce kafin tattara rahoton, sai da Hukumar Kididdigar ta gudanar da bincike tare da hadin gwiwar Majalisar Dinkin Duniya da Hukumar Bada Agajin Gaugawa ta Kasa, NEMA.

Binciken dai ya maida hankali ne a kan jihohin Anambra da Bayelsa da Delta da Jigawa da Kogi da kuma Nasarawa, sai dai alkaluman sun nuna cewa jihar Jigawa ce ta fi shan wahala, ganin yadda ambaliya ta shafi sama da kashi 90 cikin 100 na magidanta a jihar.

Adeniran, ya ce ambaliyar ruwan ta kuma yi wa harkokin kauswanci tu’annati, tare da katse wasu muhimman ayyuka, amma bangaren noma ne ya fi tagayya.