Home Labarai Man Utd Na Son Frank, Chelsea Na Cikin Tsaka Mai Wuya

Man Utd Na Son Frank, Chelsea Na Cikin Tsaka Mai Wuya

32
0

Kungiyar Manchester United na son dauko kocin Brentford,
Thomas Frank domin maye gurbin Erik ten Hag a Old
Trafford a karshen kaka, a madadin kocin Ingila Gareth
Southgate.

Sai dai akwai rahotanni da ke cewa masu kungiyar Sir Jim atcliffe da Ineos na duba yiwuwar fito da tsarin bai wa, Ten
Hag damar cigaba da tafiyar da kungiyar a sabon kaka, bisa sharadin wasu tsare-tsare na iya maye gurbinsa idan bukata ta taso.

Tottenham na fatan cimma yarjejeniya na dindindin da dan wasan RB Leipzig da Jamus Timo Werner, mai shekaru 28.

A nata bangaren kuwa kungiyar Arsenal na shirin bada kudaden alawus na fam miliya 51 da kungiyar Chelsea ta bukata kan dan wasan Sporting Lisbon da Ivory Coast, Ousmane Diomande, mai shekaru 20.

Dan wasan Norway, Erling Haaland, mai shekara 23 na shirin nuna bajinta a fafatawar da Manchester City za ta yi na kwata final da Real Madrid, a kokarin sake sayar da kansa saboda gaba a Sifaniya.

Leave a Reply