Home Labaru Ilimi Malaman Kwalejojin Fasaha Sun Shiga Yajin Aiki A Jihar Bayelsa

Malaman Kwalejojin Fasaha Sun Shiga Yajin Aiki A Jihar Bayelsa

94
0

Kungiyar Malaman Makarantun Kimiyya da Fasaha reshen
Kwalejin Kimiyya ta Tarayya ta Ekowe a Jihar Bayelsa, ta
umarci ‘ya’yan ta su shiga yajin aikin sai baba-ta-gani daga
ranar Litinin mai zuwa, saboda rashin aiwatar da ƙarin
matsayi da alawus-alawus na koyarwa da kuma rashin kyan
yanayin aiki.

Sanarwar ta fito ne da ga shugaban kungiyar Comrade Agada Franklin da babban sakataren kungiyar Justin Ikirigo da su ka raba wa manema labarai a birnin Yenagoa.

Kungiyar ta ce ta ɗauki matakin shiga yajin aikin ne a wani taron gaugawa da ta gudanar a kan wasu batutuwa da ke da matukar illa ga ‘yan kungiyar.

Ta ce shiga yajin aikin ya zama dole, saboda kungiyar ta taɓa dakatar da yajin aikin gargaɗi a watan Agusta na shekara ta 2022, sannan ta fitar da tunatarwa a ranakun 6 ga watan Disamba na shekara ta 2022 da kuma 10 ga watan Maris na shekara ta 2023.

Leave a Reply