Malaman addinin musulunci a Nijeriya sun soma fitowa su na
rokon gwamnatin Trayya kan ta dau matakin rage kudin
kujerar hajjin bana bayan karin kusan miliyan biyu da ya tada
hankulan maniyyata a fadin Nijeriya.
Kiran malaman na zuwa ne kwana guda da hukumar alhazan Najeriya NAHCON ta sanar da karin kudin, wanda malaman ke cewa dole a sauƙaƙawa maniyyata, da basu farashin dala mai sauƙi don su sami damar zuwa sauke farali a kasa mai tsarki.
Shiekh Tijjani Bala Ƙalarawi na daga cikin wadanda su kayi wannan kiran, inda ya ce ya kamata Malamai su haɗu domin yi wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu magana domin ya duba lamarin maniyyata.
A karshe, malamain addinin ya ce an san halin da kasa ke ciki da ma duniya baki daya, amma alhazan nan da za su je aikin hajji za u yi wa kasa addu’a ne, gami da fatan hadin kan malamai a fadin Nijeriya.