Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Makamashi: An Shiga Yini Na Uku Da Katsewar Wutar Lantarki A Wasu Jihohin Nijeriya

Akalla kwanaki uku kenan da wasu birane a Nijeriya su ka shiga duhu sakamokon lalacewar tushen wutar lantarki.

Akalla kwanaki uku kenan da wasu birane a Nijeriya su ka shiga duhu sakamokon lalacewar tushen wutar lantarki.

Bayanai na nuni da cewa, an samu matsala ne a manyan cibiyoyin samar da wutar, inda adadin wutar da za a iya rabawa ta sauko kasa ainun.

Kamfanoni 12 ne kawai ke aikin sarrafa wutar lantarki a Nijeriya, bayan samun raguwar Ƙarfin wutar daga megawatts dubu 3 zuwa dubu 1 da 758.

Wani jami’in daya daga cikin kamfanonin samar da wutar lantarki, ya ce an samu rugujewar na’urorin wutar lantarki da dama a ranar Talatar da ta gabata, daga tasoshin wutar lantarkin da ke amfani da iskar gas a lokacin da ake kokarin samar da wuta zuwa birnin tarayyar kasar Abuja ta hanyoyin tashoshi uku da ake da su, wadanda su ka hada da magudanan ruwa na Kainji, da Jebba da Shiroro.

Binciken kamfanoni 12 da ke samar da wutar lantarkin ya yi nuni da cewa, na’urorin sun yi ta aiki a kan megawatts dubu 1 da 758 kafin daga bisani su ka dauke gaba daya, lamarin da ya haifar da daukewar wutar.

Exit mobile version