Home Labaru Majalisar Wakilai Za Ta Binciki Ayyukan Da Aka Ki Kammalawa

Majalisar Wakilai Za Ta Binciki Ayyukan Da Aka Ki Kammalawa

1218
0
Korafi: Majalisar Dattawa Ta Gayyaci Fashola Domin Yin Bayanai A Kan Wasu Aikace-Aikace
Korafi: Majalisar Dattawa Ta Gayyaci Fashola Domin Yin Bayanai A Kan Wasu Aikace-Aikace

Majalisar wakilai ta yanke shawarar kafa kwamitin da zai binciki dukkan ayyukan raya kasa na Gwamnatin Tarayya da aka fara ba a karasa ba tun daga shekara ta 1999 zuwa yau.

Dan majalisa Francis Uduyok ya gabatar da kudiri a zaman majalisa na ranar Larabar da ta gabata, wanda Mataimakin Shugaban Majalisar wakilai Idris Wase ya shugabanta.

Da ya ke gabatar da kudirin, Uduyok ya nuna rashin jin dadi da bacin rai, ganin yadda gwamnatin tarayya ke bada kwangiloli alhali da yawan su ba a kammala ba tun daga shekara ta 1999.

Dan Majalisar, ya ce akwai ayyukan raya kasa sama dubu 20, wadanda an biya akalla kashi 50 cikin 100 na kudin da yawan su ya haura biliyoyin naira tun kafin ma a fara su.

Ya ce akwai ayyukan da aka ki kammalawa, wadanda su ka hada da madatsun ruwa da asibitoci da gine-gine da gadoji da masana’antun karafa da tituna masu yawa.

Majalisar, ta kuma nuna damuwa a kan ayyukan da aka ki kammalawa, ta na mai nuni da cewa sun kawo wa tattalin arziki cikas, domin a yanzu kudin kammala su ya rubanya.

Leave a Reply