Home Coronavirus Majalisar Wakilai Ta Gama Hutun Da Ta Tafi Bayan Barkewar Annobar Covid-19

Majalisar Wakilai Ta Gama Hutun Da Ta Tafi Bayan Barkewar Annobar Covid-19

486
0
Majalisar Wakilai Ta Gama Hutun Da Ta Tafi Bayan Barkewar Annobar Covid-19
Majalisar Wakilai Ta Gama Hutun Da Ta Tafi Bayan Barkewar Annobar Covid-19

Majalisar waikilai ta tsaida ranar Talata 28 ga watan Afrilu a matsayin ranar da za ta koma bakin aiki, bayan hutun da ta tafi sakamakon barkewar annobar COVID-19.

A cikin wata sanarwar da majilisar ta aikawa mambobin ta, mai dauke da sa hannun magatakardar majalisar Patrick A. Giwa, ta ce an shawarci sauran hadiman majalisa su cigaba da gudanar da ayyukan su daga gida.

Sanarwar ta kara da cewa, za a yi zaman majalisar ne bisa biyayya ga shawarwarin hukumar NCDC da kuma wasu sabbin matakai da majalisa ta dauka.

A cewar Sanarwar, za a sanar da dukkan mambobin majalisar wakilai cewa za a dawo zaman majalisa a ranar Talata, 28 ga watan Afrilu, da misalin karfe 10:00 na safe, tare da  shawartar mambobin su kiyaye sabon lokacin da aka bayyana a matsayin ranar dawowa daga hutu.

Leave a Reply