Majalisar Dokoki ta Jihar Kaduna, ta dakatar da wasu
Shugabannin Kananan Hukumomi uku bisa zargin karkatar da
wasu kudade.
Kananan Hukumomin da aka dakatar da Shugabannin su uwa sun hada da Kaura da Kagarko da kuma Chikun.
An sanar da dakatarwar ne bayan an zargi shugabannin da bada kwangiloli ba tare da bin ka’idojin da su ka dace ba.
Kwamitin wucin gadi a kan binciken a karkashin jagorancin ‘yar majalisa mai wakiltar yankin Lere ta Gabas Munirat Sulaiman Tanimu, ya yi nazari a kan harkokin kudin kananan hukumomi biyar, wadanda su ka hada da Chikun da Kaura da Kagarko da Soba da Birnin Gwari.
Majalisar dai ta bada umarnin gudanar da binciken ne bayan wani kuduri da aka cimmawa a ranar 18 ga watan Yuli na shekara ta 2023.
Munirat Sulaiman Tanimu, ta ce kwamitin ya gayyaci shugabannin da abin ya shafa domin su samar da takardun kudi da su ka hada da bayanan banki daga watan Yuni na shekara ta 2022 zuwa watan Yunin shekara ta 2023, da asusun ajiya na DVA da aka amince da kasafin kudin shekara ta 2022 da 2023, da kuma bayanan kwangilolin da aka bada matakan kammala su da dai sauran su.