Home Labarai Majalisar Dokokin Bauchi Ta Amince Da Dokar Kafa Jami’ann Tsaro Mallakin Jihar

Majalisar Dokokin Bauchi Ta Amince Da Dokar Kafa Jami’ann Tsaro Mallakin Jihar

99
0

Majalisar Dokoki ta Jihar Bauchi, ta amince da wata doka da za ta bada damar samar da jami’an tsaro mallakar jihar domin magance kalubalen tsaro.

Gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed ya bayyana haka, lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan wani dattijo mai suna Jauro Dakkuna, wanda ‘yan bindiga su ka kashe a yankin Shafa da ke Karamar Hukumar Alkaleri.

Gwamna Bala Mohammed, ya ce gwamnatin jihar Bauchi ta na shirin daukar matasa sama da dubu 2 aikin tsaro a jihar, ya na mai cewa, babu yadda za a yi wani ya taso daga jihar Zamfara ya yankin Shafa don ya kashe wani sai dai idan ya na da mai taimaka ma shi.

Ya ce kamar yadda hukumomin tsaro su ka saba fada, irin wannan abu ba zai iya faruwa ba sai an hada kai da wasu a cikin al’umma.

Bala Mohammed, ya kuma shawarci jama’a su ba gwamnatin jihar Bauchi bayanai ta hannun shugabannin kananan hukumomi da Kansiloli da masu unguwanni domin daukar matakin gaugawa domin dakile duk wata barazanar tsaro.