Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Majalisar Dinkin Duniya Za Ta Tunkarari Matsalar Yunwa A Arewa Maso Gabas

Majalisar Dinkin Duniya, ta kebe zunzurutun kudi Dala miliyan 20, kwatankwacin Naira miliyan dubu goma sha uku da miliyan dari biyu domin tunkarar kalubalen matsalar abinci a yankin Arewa maso gabashin Nijeriya

Jagoran ayyukan jin-kai na majalisar a Nijeriya Mathias Schmale ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja, inda ya yi gargadin cewa dole ta sa aka dauki matakin, duba da irin ja’ibar yunwar da za a fuskanta sakamakon rikicin da ya ki ci yaki cinyewa a yankin.

Mista Mathias, ya ce za a kuma samar da kudaden ne daga asusun ayyukan jin-kai na Nijeriya da asusun tunkarar bukatu na gaugawa, ya na mai cewa matsalar abinci mai gina jiki ga yara a yankin arewa maso gabas ta ninka irin wadda ta faru a bara sau biyu, ko kuma ninki hudu na wanda ya faru shekaru biyu a baya.

Kawo yanzu dai kimanin mutane dubu dari biyar ne aka kiyasta za su fuskanci matsananciyar yunwa a jihohi uku na yankin arewa maso gabashin Nijeriya.

Exit mobile version