Majalisar dattawa ta amince da naɗin mutane 20 da shugaba
Tinubu ya aike mata domin amincewa da su a matsayin
mashawartan sa.
Matakin dai ya na zuwa ne, bayan da shugaba Tinubu ya aike wa majalisar wasiƙar neman amincewa domin ya naɗa mutanen.
Sai dai a wasiƙar da shugaban majalisar Sanata Ahmad Lawan ya karanto babu sunayen mutanen a ciki.
Ana dai kallon sabbin naɗe-naɗen da shugaba Tinubu zai yi a matsayin wata manuniyar inda alƙiblar gwamnatin shi za ta fuskanta wajen magance tarin matsalolin da Nijeriya ke fuskanta.
You must log in to post a comment.