Kudirin neman samun damar Najeriya ta koma kan tsohon taken ta ya tsallake karatu na 2 a Majalisar Dattawa.
Kudirin da daya daga cikin jagororin majalisar, Opeyemi Bamidele ya gabatar ya samu gagarumin goyon baya daga ‘yan majalisar.
An mika kudirin zuwa ga kwamitocin majalisar kan Bangaren Shari’a da na kare hakkin dan Adam da kuma na harkokin shari’a, inda aka bukaci su dawo da rahoto akan sa cikin mako 2.
‘Yan majalisar wadanda da alama galibin su na goyon bayan kudirin, sun kafa hujja da cewar, tsohon taken zai dabbaka hadin kai,
da zaman lafiya da bunkasar arzikin kasa, sabanin wanda ake amfani dashi a halin yanzu.
Bayan wata ganawar sirrin da aka tafka mahawara akan kudirin, ‘yan majalisar sun ce taken Najeriyar da ake amfani da shi a halin yanzu gwamnatocin mulkin soji ne suka samar da shi ta hanyar irin nasu dokokin,
don haka kamata ya yi a yi watsi da shi domin shigar da akidu da muradun tsarin dimokradiyar Najeriya musammam kara jaddada akidar kasa daya al’umma daya.
An maye gurbin tsohon taken daya soma da “Nigeria We Hail Thee” a turance da wanda ya soma da “Arise O’ Compatriots” a shekarar 1978.