Majalisar Dattawa na shirin kafa wata hukuma da za ta rika kula da bayanai ta kasa, wadda za ta daidaita ayukan hukumomi yadda suka dace.
Dan majalisar dattawa mai wakiltan shiyyar Taraba ta tsakiya kuma shugaban kwamitin kula da manyan ayuka na majalisar Yusuf Abubakar Yusuf, ne ya gabatar da ita a gaban majalisar.
Yace dokar zata manufar taimaka wajen kafa hukumar da za ta inganta kimar Najeriya a idon duniya ta hanyar kirkira da kiyayewa da sabunta bayanai da kidayar kamfanoni a Najeriya, da kuma samar da tsari mai inganci don daidaita ayukan hukumomi da suka shafi kasuwanci.
Yayin da yake bayani kan yadda hukumar za ta gudanar da aiyukan ta, Sanata Yusuf Abubakar ya ce duk bayanai da za su fito daga Gwamnati, ya kamata su zama bayanai sahihai.
Yusuf ya ba da misali cewa idan aka nemi sanin yawan man fetur da ake hakkowa daga Najeriya, za a tambayi ma’aikatar man fetur ta kasa da ofishin kididdiga amma za’a iya samun alkaluma daban-daban, saboda haka wannan hukuma ita ce za ta daidaita bayanai na gaskiya da zai sa kasashen duniya irin su Amurka da Ingila da kasar China su amince ta bayanan.