Majalisar Dattawa ta amince da yin garambawul a kundin dokokin zaɓe na shekara ta 2022, domin a ba Wakilai masu rike da kujeru damar yin zaɓe a tarurrukan jam’iyyun siyasa.
Idan dai ba a manta ba, kundin da shugaba Buhari ya
sanya wa hannu ya hana rukunin Wakilan yin zaɓe a
zaɓubukan fidda gwani.
Rukunin Wakilan dai ya kunshi Kansiloli da shugabannin
kananan hukumomi da shugabannin jam’iyya na kananan
hukumomi da ‘yan majalisun jihohi da na tarayya.
Sauran sun haɗa da gwamnoni da mataimakan su da
shugaban ƙasa da mataimakin sa, da ‘yan kwamitin
gudanarwa na jam’iyyun siyasa da shugabannin jam’iyyu
na jiha da Sakatarorin su.
Shugaban majalisar Dattawa Sanata Ahmed Lawan, ya ce
akwai bukatar gaggauta gyara a kan sashen tun kafin a
fara zabubukan fidda ‘yan takara.