Home Labarai Majalisar Dattawa Ta Nemi Sojoji Su Toshe Hanyoyin Da ‘Yan Bindiga Ke...

Majalisar Dattawa Ta Nemi Sojoji Su Toshe Hanyoyin Da ‘Yan Bindiga Ke Tserewa

212
0

‘Yan majalisar dattawa sun umarci sojoji da sauran jami’an tsaro su sa ido tare da toshe hanyoyin da ‘yan ta’adda ke bi su na tserewa domin hana su komawa wasu sassan kasar nan.

Majalisar ta bada umarnin ne bayan gabatar da kuduri da Sanata
Aliyu Sabi Abdullahi na jihar Neja ya yi, sakamakon sabbin
hare-hare da satar mutanen da ake yi a yankunan kananan
hukumomin Mariga da Mashegu da Kontagora da kuma Borgu.

Sanatan, ya ce sakamakon muggan hare-haren da sojoji da
sauran jami’an tsaro ke kai wa ‘yan ta’addan da su ka addabi
yankunan gabashin jihohin Sokoto da Zamfara, ‘yan ta’adda su
na ta tserewa zuwa jihar Naija.

Ya ce ya kamata a tsara hare-haren da ake kai wa ‘yan ta’addan
yadda ya kamata, ta yadda za a toshe duk wata hanya da su ke bi
su na shiga sassan jihar Neja.

Majalisar Dattawa, ta kuma umarci hukumar bada agajin
gaugawa ta kasa ta samar da kayan abinci da sauran muhimman
abubuwan jin dadi ga mutanen kauyukan da hare-haren ‘yan
ta’addan ke shafa, da kuma ‘yan gudun hijira a yankunan
kananan hukumomin Mariga da Mashegu da Kontagora da kuma
Borgu.

Leave a Reply