Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Majalisar Dattawa Ta Dauki Mataki Kan Masu Zanga-Zangar Da Su Ka Kutsa Harabar Ta

Majalisar dattawa ta kafa kwamitin da zai tattauna da ƙungiyoyin ƙwadago da ke zanga-zanga, waɗanda su ka karya ƙofar shiga majalisar ta farko.

Masu zanga-zangar dai sun fara ne daga shatale-talen Fountain da ke birnin Abuja zuwa majalisar tarayya, a kan abinda su ka kira tsauraran matakan tattalin arziki na gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Bayan sun isa majalisar tarayya, masu zanga-zangar sun karya ƙofar farko ta majalisar, sannan su ka shige zuwa cikin harabar majalisar kai tsaye.

Shugaban majalisar dattawa Sanata Godswill Akpabio ya shiga ganawa da sanatoci a keɓance, inda bayan ya fito ya ce majalisar ta kafa kwamitin mutane uku domin tattaunawa da masu zanga-zangar.

Kwamitin dai zai kasance ne a ƙarƙasin jagorancin mai tsawatarwa na majalisar Dattawa Sanata Ali Ndume, yayin da da sauran ‘yan kwamitin su ka hada da Sanata Ireti Kingibe da Sanata Tony Nwonye, kuma tuni sun gana masu zanga-zangar a majalisar tarayya.

Exit mobile version