Home Labaru Majalisar Dattawa Ta Ɗaga Darajar Kwalejin Fasaha Zuwa Jami’A A Jihar Kwara

Majalisar Dattawa Ta Ɗaga Darajar Kwalejin Fasaha Zuwa Jami’A A Jihar Kwara

114
0

Majalisar dattawa ta amince da kafa makarantar koyar da ilimin ma’adanan ƙasa da ilimin halitta a Guyuk.

Haka kuma, majalisar ta amince da ɗaga darajar kwalejin fasaha ta Offa da ke jihar Kwara, daga mai bada matakin karatu na Diploma zuwa Jami’a mai bada takardar shaidar kammala matakin Digiri, ta kuma sake amincewa da kudirin jami’o’in fasaha na tarayya na shekara ta 2004 aka yi wa garambawul.

Majalisar dattawa dai ta amince da waɗannan kudirorin ne, biyo bayan nazarin da ta yi a kan rahotanni biyu da kwamitin hukumar inganta manyan makarantu TETFUND da na makarantun gaba da Sakandire su ka gabatar mata.

Shugaban kwamitin Sanata Ahmad Babba Kaita, ya ce kafa makarantar koyar da ilimin ma’adanai da ilimin halittun ƙasa zai taimaka wajen samar da horo da kwarewar kayan aiki ga sashen ma’adanai.

Ya ce makarantar za ta haɗa hannu da wasu manyan makarantun duniya, wajen ci-gaban ilimin da kuma ƙarfafa wa malaman makaranta gwiwa wajen aikin su tare da ba su horo.