Home Home Majalisar Dattawa Ba Ta Amince Da Aika Sojoji Zuwa Kasar Nijar Ba

Majalisar Dattawa Ba Ta Amince Da Aika Sojoji Zuwa Kasar Nijar Ba

56
0

Majalisar dattawa ta ce ba za ta amince wa Shugaba Tinubu ya tura sojojin Nijeriya zuwa kasar Nijer ba, bisa wasu muhimman dalilai da sai Majalisar ta yi zama na musamman akan su.

A cikin wasikar da Shugaba Tinubu ya aikr wa Majalisar dai, ya nemi goyon bayan su a kan matakin da Kungiyar ECOWAS ta dauka ciki har da tsoma baki a kan maido dimokradiyya a kasar Nijar.

Bayan karanta wasikar da Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya yi, sai Sanata Abdul Ningi ya kawo kuduri na jan hankalin Majalisar game da bukatar Tinubu.

Sanata Ningi ya ce yaki ba abin wasa ba ne, musamman yakin da ya hada da iyaka, domin a yankin Arewa akalla jihohi bakwai ne su ka hada iyaka da kasar Nijar.

Ya ce abu ne mai wuya mutum ya banbanta ‘yan asalin Nijar da ‘yan Nijeriyar da ke kan iyaka, don haka dole ne Majalisa ta yi taka tsantsan, ya na mai cewa shugaban kasa ba ya da hurumin daukar wannan matakin shi kadai ba tare da ya kawo dalilan sa a gaban majalisa ba.

Sanata Ali Ndume, ya ce dokar kasa ba ta ba Majalisa damar ta amince da wannan matakin ba, kuma doka ba ta ba shugaban kasa hurumin yin gaban kan sa ba.

Leave a Reply