Home Coronavirus Majalisa Za Ta Binciki Zargin Badakala Naira Biliyan 40 A Hukumar NDDC

Majalisa Za Ta Binciki Zargin Badakala Naira Biliyan 40 A Hukumar NDDC

6402
0
Majalisa Za Ta Binciki Zargin Badakala Naira Biliyan 40 A Hukumr NCDC
Majalisa Za Ta Binciki Zargin Badakala Naira Biliyan 40 A Hukumr NCDC

Majalisar wakilai za ta fara bincike a kan zargin da ake yi na cewa, an tafka badakala a hukumar kula da cigaban yakin Neja delta NDDC.

Kawo yanzu dai, majalisar ta aikawa ministan harkokin Neja-Delta, Godswill Akpabio da ‘yan kwamitin rikon kwaryar hukumar takarda gayyata domin amsa wasu tambayoyi a majalisar.

Majalisar wakilai dai, t na zargin an wawuri wasu makudan kudade a hukumar NDDC, wacce take karkashin kulawar sanata Godswill Akpabio.

Haka kuma, majalisar ta bukaci kwamitin da ke sa ido a kan harkokin Neja-Delta ya binciki zargin karkatar da Naira biliyan 40 da aka ce an kashe a cikin watanni biyu zuwa uku, tare da gabatar da  rahoton binciken a kan lokaci.

‘Yan majalisar sun cimma wannan matsaya ne bayan dan majalisa Peter Akpatason ya kawo da kudirin a zaman majalisar na ranar talatar da ta gabata.

A karshe majalisar ta yanke hukuncin kiran Godswill Akpabio da shugabannin hukumar NDDC na rikon kwarya domin su yi wa ‘yan Nijeriya bayanin aikin da su ke yi da kudaden.