Home Home Majalisa Za Ta Binciki Sojojin Ruwa Bisa Ƙone Jirgin Da Suka Kama...

Majalisa Za Ta Binciki Sojojin Ruwa Bisa Ƙone Jirgin Da Suka Kama Da Ɗanyen Man Sata

387
0
Majalisar Wakilai ta yanke shawarar binciken jami’an Rundunar Sojin Ruwa, bisa zargin su da banka ma wani jirgin ruwa da su ka kama maƙare da ɗanyen mai na sata wuta.

Majalisar Wakilai ta yanke shawarar binciken jami’an Rundunar Sojin Ruwa, bisa zargin su da banka ma wani jirgin ruwa da su ka kama maƙare da ɗanyen mai na sata wuta.

Wannan dai ya biyo bayan amincewa da ƙudirin gaugawa a kan muhimmancin kasa da ɗan majalisar wakilai Onofiok Luke ya gabatar a zaman majalisar na ranar Larabar da ta gabata a Abuja.

Onofiok Luke ya gabatar da cewa, matsalar satar man fetur matsala ce da ta daɗe a yankin Neja Delta, kuma ta haifar da mummunar lalacewar muhalli a yankin.

Ya ce lamarin ya yi illa ga samar da kuɗaɗen shigar Nijeriya, wanda ya sa ta yi asarar gangar ɗanyen mai dubu 470 a kowace rana, wanda ya kai kiyasin Dala miliyan 700 duk wata. Tuni dai Majalisar ta yanke shawarar gudanar da bincike a kan lalata jirgin da jami’an tsaron su ka yi maimakon ajiye shi a matsayin shaidar kotu.

Leave a Reply