Home Labaru Majalisa Za Ta Binciki Sanata Elisha Abbo

Majalisa Za Ta Binciki Sanata Elisha Abbo

599
0
(L) Sanata Ahmad Lawan, Shugaba Majalisar Dattawa (R) Sanata Uba Sani

Shugaba majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawan, ya kafa kwamitin musamman domin binciken bidiyon da ya yadu a kafofin sada zumunta na zamani, wanda ke nuna sanata Elisha Ishaku mai wakiltar mazabar Adamawa ta kudu ya na dukan wata mata.

Matakin dai ya biyo bayan korafin da Sanata Uba Sani ya gabatar a zauren majalisa, inda ya bayyana yadda abin ke janyo ce-ce-ku-ce a fadin Nijeriya da ma duniya baki daya.

Sanata Uba Sani, ya bukaci majalisar dattawa ta dauki matakin hukunta Sanata Elisha Abbo a kan wannan abin kunyan da ya aikata, wanda ka iya bata wa majalisar suna a idon duniya.

Sai dai Shugaban majalisar ya ce wannan zargi ne tukunna, don haka sai an gudanar da bincike kafin a tuhume shi.

Ya ce ya samu kiraye-kiraye da dama daga ciki da wajen Nijeriya a kan abin da ya faru, don haka sakamakon wadannan kiraye-kiraye da bacin ran da ‘yan Nijeriya su ka nuna, ya na kafa kwamitin binciken zargin zaluncin da ake yi wa Sanata Elisha Abbo.