Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Majalisa Ta Zargi Muhammadu Buhari, Sanatoci Za Su Binciki Tsohuwar Gwamnati

Majalisar dattawa ta ce za ta gudanar da bincike a kan
kwangilar aikin Gas da aka ba kamfanin ‘Acugas Limited’ a
lokacin gwamnatin Muhammadu Buhari.

Sanata Aniekan Bassey daga jihar Akwa Ibom ne ya gabatar da bukatar hakan a zauren majalisar, inda ya ce a shekara ta 2017 ne kamfanin lantarki na NDPHC ya shiga yarjejeniyar Dala miliyan 10 da kamfanin Acugas Limited domin samar da Gas.

Ya ce wadda ta sa hannu domin a ba kamfanin Calabar Generation Gas din ita ce Zainab Ahmed, a lokacin da ta ke Ministar kudi da tattalin arziki.

Sanatan ya kara da cewa, makudan biliyoyin da aka batar ya jawo abin magana, kuma ana zargin akwai nuku-nuku wajen yadda aka biya kwangilar, don haka ya bukaci idan an kafa kwamitin harkar lantarki a bankado gaskiyar abubuwan da su ka faru wajen bada kwangilar, kuma ya kamata a gayyaci duk wani ko hukuma da ke da hannu a kwangilar domin a ji ta bakin su.

Exit mobile version