Home Labaru Ilimi Majalisa Ta Dakatar Da JAMB Daga Hukunta Dalibar Da Ta Yi Sakamakon...

Majalisa Ta Dakatar Da JAMB Daga Hukunta Dalibar Da Ta Yi Sakamakon Bogi

122
0

Majalisar wakilai ta sa baki a batun zargin da hukumar shirya
jarabawar share fagen shiga jami’a ta JAMB ta yi ma wata
daliba mai suna Mmesoma Ejikeme na kirkirar sakamakon
bogi.

‘Yan majalisar sun nuna damuwa a kan yadda hukumar JAMB ta gaza nuna dattako a kan lamarin da ya shafi karamar yarinya, ta hanyar janye sakamakon jarabawar ta tare da dakatar da ita na tsawon shekaru uku.

Tuni dai majalisar ta kafa kwamitin da zai binciki lamarin, tare da neman hukumar JAMB ta dakatar da zartar da hukunci har sai ta kammala bincike.

Idan dai ba a manta ba, a ranar Lahadin da ta gabata ne hukumar JAMB ta zargi dalibar da kirkirar sakamakon bogi a jarabawar wannan shekarar.

Leave a Reply