Home Labaru Majalisa Ta 9: An Ki Tantance Rochas Okorocha A Wajen Bikin Rantsarwa

Majalisa Ta 9: An Ki Tantance Rochas Okorocha A Wajen Bikin Rantsarwa

604
0

Tun da misalin karfe 7 da minti 40 na safe tsohon gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha ya isa harabar majalisar dokoki ta tarayya gabannin bikin rantsar da ‘yan majalisar.

Idan dai za’a iya tunawa, an kaddamar da Okorocha a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar dan majalisar dattawa ta mazabar Imo ta yamma, amma hukumar zabe ta ki ba shi takardar shaidar cin zaben.

Sai dai wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi umurnin cewa a ba Okorocha takardar shaidar cin zaben sa a makon da ya gabata.

Rahotanni sun ce hukumar majalisar dokoki ta kasa ba ta tantance Rochas Okorocha domin ya samu damar halartar bikin rantsarwar ba.

Har yanzu dai hukumar ba ta cika umarnin kotu ba, yayin da ake shirin rantsar da majalisa ta tara, inda hukumar zaben ta ce ta na duba lamarin ne tukunna.

Leave a Reply