Mun samu labarin rasuwar dan majalisar mai wakiltar mazabar Chikun da Kajuru daga jihar Kaduna, Hon. Ekene Adams, dan jam’iyyar Labour.
Marigayi Hon. Ekene Adams ya rasu ne yana da shekaru talattin da tara a duniya.
Dan majalisar kafin rasuwar sa she ne shugaban kwamittin wasanni, kuma wannan she ne karo na farko da ya zo majalisar ta wakilai.
Marigayi Ekene Adams dai mutane sun shaida mutun ne mai taimakon jama’a da son ci gaban matasa da harkar wasanni a Najeriya.
Rasuwar Adams, ita ce ta biyu a Majalisar Wakilai cikin mako guda, bayan rasuwar Hon. Olaide Akinremi (Jagaban) daga Jihar Oyo a ranar 10 ga Yuli.