Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Mahara Sun Yi Garkuwa Da Jami’in Civil Deffence Da ‘Ya’yan Sa Biyu A Abuja

Dagacin kauyen Dafara da ke karamar hukumar Kuje a birnin tarayya Abuja Makeri Joseph, ya ce wasu mahara sun kashe mutum daya, sannan sun waske da ma’aikacin hukumar tsaro ta farar hula Civil Deffence da ‘ya’yan sa biyu.

Joseph ya bayyana wa manema labarai cewa, lamarin ya faru ne a makon da ya gabata, kuma shi ne karo na biyu da ake garkuwa da mutane a karamar hukumar Kuje.

Idan dai ba a manta ba, a ranar Litini ta makon da ya gabata, wasu ‘yan bindiga sun sace mutane tara bayan sun harbe wani Jami’in tsaro na Civil Deffence.

A cikin wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan Abuja ta raba wa manema labarai, kakakin rundunar Anjuguri Manzahp ya ce rundunar ta hada hannu da sauran jami’an tsaro don ganin an ceto mutanen da aka sace.

Exit mobile version