Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Mahara Sun Kashe Mutum 22 A Sokoto

Mahara dauke da muggan makamai sun kashe mutum 22 a jihar Sokoto.

‘Yan bin digar sun kuma jikkata wasu da dama a harin da suka kai kauyen Gangara da ke karamar hukumar Sabon Birni, sun kuma jikkata mutane da dama.

Rundunar ‘yan sandan jiahr Sokoto ta tabbatar da aukuwar harin na ranar Laraba.

Kakakin ‘yan sandan jiahr Mohammed Abubakar Sadiq, ya ce ‘yan bindigar sun yi kokarin yi wa soji da ‘yan sandan da suka je domin su fatattake su daga kauyen tirjiya.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ibrahim Sani Ka’oje, ya ba da umurni a yi bincike domin gano ainihin abin da ya faru a kauyen.

Exit mobile version