Home Home Mahaifiyar Abubakar Sheƙau Ta Ce Ya Jefa Ta Cikin Ƙunci

Mahaifiyar Abubakar Sheƙau Ta Ce Ya Jefa Ta Cikin Ƙunci

65
0

Mahaifiyar tsohon shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ta ce ba ta da masaniya ko ya na da ‘ya’ya ko babu.

Fatima Abubakar ta bayyana haka ne, yayin wata hira da gidan talabijin Trust TV ya yi da ita, inda ta ce ko Shekau ya na raye ko mace babu wani abu da ke tsakanin ta da shi.

Ta ce Shekau ya jefa ta cikin ukuba har ta kai ga ta cire rai da shi, ta na mai cewa duk da ita ta tsugunna na haife shi tuni sun raba jiha da shi.

Fatima Abubakar, ta ce ba ta taba sanin ko Shekau ya na da ‘ya’ya ko babu ba, amma a yadda ya jefa ta cikin bakin ciki Allah zai yi hisabi a tsakanin su ranar gobe kiyama.