Home Labaru Mafi Karancin Albashi :Gwamnati Ba Za Ta Iya Cutar Ma’aikata Ba ...

Mafi Karancin Albashi :Gwamnati Ba Za Ta Iya Cutar Ma’aikata Ba Inji – Tuc

342
0

Kungiyar kwadago ta TUC, ta tabbatar wa ma’aikata cewa ya zama dole gwamnatin tarayya ta kaddamar da mafi karancin albashin Naira 30,000.

Shugaban kungiyar Bobboi Kaigama ya bayyana haka a birnin Akure na jihar Ondo, yayin wani taron musamman da kungiyar ta shirya, inda ya ce zancen mafi karancin albashi ba maganar yaudara ba ce.

Shugaban wanda sakataren kungiyar Musa Lawal ya wakilta, ya ce shugaban kasa ya fitar da kwamitin kwararru a kan duba lamarin mafi karancin albashin domin a kaddamar da shi.

Kaigama ya shaida wa ma’aikata cewa, su na bin diddigi don ganin yadda lamarin zai kasance, domin bukatar su ita ce kada ya kasance an samu tangarda ko kadan.

Leave a Reply