Home Labarai Machina Ya Yi Wa Shugaban Jam’Iyyar APC Kakkausan Raddi

Machina Ya Yi Wa Shugaban Jam’Iyyar APC Kakkausan Raddi

92
0

Dan takarar kujerar Sanata a karkashin jam’iyyar APC Bashir Sheriff Machina, ya maida wa shugaban jam’iyyar na kasa Sanata Abdullahi Adamu martani a kan wasu kalamai da ya yi.

Sheriff Machina ya ce ya na neman hakkin sa ne a jam’iyyar APC, domin ba ya fada da Sanata Ahmad Lawan ko wani, don haka ya ce bai dace dattijo kamar Sanata Abdullahi Adamu ya rika fadin maganganu masu zafi a kan shi ba.

Machina ya gargadi Sanata Abdullahi Adamu da cewa, ya guji tsoma masu baki a harkokin siyasar jihar Yobe.

Ya ce Ahmad Lawan da aka mika wa hukumar zabe sunan sa ba ya cikin ‘yan takarar jam’iyyar APC a zaben fidda gwanin da aka yi, kuma a cewar sa, duk wani dan Nijeriya ya ga sakamakon zaben da aka fitar cewa Ahmed Lawan bai yi takara ba.

Machina ya kara da cewa, ya kamata Sanata Adamu ya tsaya matsayinsa na shugaban APC na kasa, ba shugaban wata kabila ko wanni bangare ba.