An samu jinkirin tashin jirage zuwa ƙasashen waje a filin tashi da saukar jiragen sama na Murtala Muhammad da ke Lagos, inda ma’’aikatan kamfanonin jiragen sama na Nijeriya su ka sanar da shiga yajin aiki saboda buƙatar ƙarin albashi.
Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ruwaito cewa, kamfanonin jiragen Air Peace da Dana Air sun jinkirta tashin jiragen su.
Wani hoton bidiyo ya nuna fasinjoji tsaye cikin dogayen layuka, inda aka ji wanda ya ɗauki bidiyon ya na cewa abubuwa ba su tafiya yadda ake bukata.
Tuni dai hukumomin filin jirgin saman su ka wallafa sako a shafin su na twita, inda su ke cewa abubuwa za su kyautatu, sai dai za a samu jinkirin tashin jirage.