Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Ma’Aikatan Kaduna Za Su Kwankwadi Lagwada A Ƙarkashin Mulki Na – Uba Sani

Zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani, ya yi
alkawarin shimfida wa ma’aikatan jihar Kaduna ababen more
rayuwa domin jin daɗin su bayan an rantsar da shi.

Uba Sani dai ya taya ma’aikatan Nijeriya da kungiyar kwadago murnar zagayowar ranar ma’aikata, ya na mai cewa sun bada gudunmawar da ba za ta iya misaltuwa ba wajen gina kasa.

Ya ce gwamnatin shi za ta yi aiki da su kafaɗa da kafaɗa, kuma zai bada fifiko da maida hankali matuka ga jin daɗin su, tare da samar da kayan aiki da duk abin da za su bukata domin jin dadin su da kuma samun nasara a aikin su.

Uba Sani ya kara da cewa, ma’aikatan Kaduna za su san ana yi da su yanzu, domin masu kwazo za su shaida ta hanyar karrama su da kuma ba su kyaututtuka, sannan zai tabbatar da jin dadin su a koda yaushe.

Exit mobile version