Home Labaru Ma’adanai: Mun Kashe Sama Da Naira Biliyan 14 Don Hako Ma’adanai –...

Ma’adanai: Mun Kashe Sama Da Naira Biliyan 14 Don Hako Ma’adanai – Gwamnati

318
0

Tsohon ministan albarkatun kasa Honarabul Abubakar Bawa Bwari, ya ce gwamnatin tarayya ta ce ta kashe sama da naira biliyan 14 domin hako ma’adanai a cikin shekaru uku.

 Abubakar Bwari, ya ce ana ci-gaba da aikin hako ma’adanan,  sannan ya bukaci duk wanda zai gaje shi ya dabbaka ayyukan da ya yi na ci-gaba.

Ya ce duk da cewa ya gamu da kalubale masu yawa a lokacin  ya na ofis, musamman matsalar isassun kudi, ma’aikatar shi ta gano wasu muhimman albarkatu da ya kamata gwamnati ta tattala su.

 
Tsohon ministan, ya ce hakan zai kara wa gwamnati kudaden shiga masu yawa kuma ya samar da aikin yi ga matasa masu zaman kashe wando.

A karshje ya ce idan aka yi hakan, za a janyo hankalin manyan ‘yan kasuwa domin ana bukatar su.

Leave a Reply