Home Labaru Ma.Aikatan Najeriya Sun Shiga Tasku Lokacin Mulkin Buhari – NLC

Ma.Aikatan Najeriya Sun Shiga Tasku Lokacin Mulkin Buhari – NLC

108
0

Kungiyar Ƙwadago ta Nijeriya NLC, ta ce ma’aikatan
Nijeriya su na cikin wani hali, kuma babu wani sauyin a zo a
gani da aka samu tun bayan kama mulkin shugaba
Muhammadu Buhari.

Sakataren ƙungiyar ƙwadago ta Nijeriya Kwamared Nasir Kabir, ya ce ci-gaba kaɗan ne kawai za a iya cewa ma’aikata sun samu a ƙarƙashin gwamnatin APC.

Ya ce abin farin ciki ne sake zagayowar ranar ma’aikata ta duniya, amma maganar gaskiya al’amuran da ma’aikata ke fuskanta a Nijeriya da abubuwan da su ke fama da su ba abin murna ko farin ciki ne ba.

Abubuwan da Kwamared Nasir ya ce su ne manyan ƙalubalen da ma’aikata a Nijeriya ke fuskanta, sun hada da tashin farashin kayan masarufi, da rashin isassun kuɗi a hannu, da biyan kuɗin makarantar yara, da tsadar wutar lantarki, da tsadar man fetur, da kuɗin kiwon lafiya.

Kwamared Nasir ya kara da cewa, ƙarancin albashin ma’aikata a Nijeriya ba zai ishi magidanci ya sayi buhun shinkafa da zai ciyar da iyalan sa ba.

Leave a Reply