Lyon da ke buga gasar League ta 1 ta Faransa ta miƙa tayin fan miliyan 12.7 domin ɗaukar ɗan wasan Ben Godfrey.
Godfrey ya koma Everton ne daga Norwich kan fan miliyan 25 a 2020, tun daga nan kuma ya buga mata wasa 93
ciki har da 16 a kakar da ta gabata.
Ɗan ƙwallon mai shekara 26 ya shiga shekarar ƙarshe ta kwantaragin sa a Goodison Park.
Ana ganin kuma zakarun gasar Europa League na bara, Atalanta, na neman ɗaukar matashin ɗan ƙasar Ingila,
wanda kuma ya buga mata wasa biyu.
Rahotonni sun ce Godfrey ya so komawa Atalanta a kakar da ta gabata kan fan miliyan 10 a watan Janairu, abin ya gagara.