Home Labaru Lokacin Gyaran Dokar Zaɓe Na Ƙara Ƙurewa – INEC

Lokacin Gyaran Dokar Zaɓe Na Ƙara Ƙurewa – INEC

125
0

Hukumar zaɓe mai zaman kan ta ta kasa INEC, ta ce ci-gaba da jinkiri wajen amincewa da dokar zabe ta shekara ta 2010 da Majalisar Dokoki ta tarayya ta yi na iya yin tasiri a kan amincewa da sabbin gyare-gyare a zaben shekara ta 2023.

Ta ce duk da cewa ta na gudanar da ayyukan ta ne bisa tsarin dokokin da ake da su, amma ya na da muhimmanci a samar da dokar da za ta jagoranci gudanar da zaben akalla watanni 12 zuwa 18 kafin a gudana da zaben.

Tuni dai Shugaban Hukumar Farfesa Mahmud Yakubu, ya bayyana 23 ga watan Fabrairu na shekara ta 2023 a matsayin ranar da za a gudanar da zaben shugaban kasa.

Gyaran dokar zaben dai ya haifar da zazzafar muhawara, musamman a kan bukatar watsa sakamakon zaben ta yanar gizo da kuma zaɓen ‘yar tinƙe ga kowace jam’iyya.