Kungiyar Likitocin ta kasa reshen jihar Kogi ta nuna damuwar ta bisa kin yi wa mutanen da ake zargin ba su da lafiya gwajin cutar COVID-19 a jihar.
A ranar Talatar da ta gabata dai, kimanin mutane dubu 20 ne aka yi wa gwajin kwayar cutar COVID-19 a fadin Nijeriya, sai dai a jihar Kogi har yanzu ba a samu labarin mai dauke da cutar ba, sakamakon yadda gwamnatin jihar ta hana ayi wa mutane gwajin cutar.
Shugaban kungiyar likitocin reshen jihar Dakta Kabir Zubair ya gargadi gwamnatin Yahya Bello, a kan matakin da ta dauka, wanda ya ce ya na da matukar hadari.
Kabir Zubair ya kuma nuna fargabar sa a kan kin yi wa mutanen gwajin cutar, wanda a cewar sa hakan zai iya zama matsala ga jihar.
Haka kum, Dakta Zubair ya ce, nan gaba kadan za a rika neman wadanda su ka kamu da cutar a rasa sakamakon yadda gwamnati jihar ta ki bari ayi wa mutane gwaji, domin killace masu dauke da cutar.
A baya dai, dhugaban cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC Chikwe Ihekweazu ya zargi jihohin Nasarawa da Cross River da Kogi bisa kin yi wa mutane gwaji, tare da cewa jihohin na kokarin boyewa duniya gaskiyar lamari a kan cutar.